1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kama mata 'yan uwan jagoran Hamas al-Arouri

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 14, 2024

Hezbollah ta ce farmakin da Amurka da kawayenta suka kai kan 'yan Houthi na Yemen zai haddasa rincabewar rikicin yankin, don haka babu gudu babu ja da baya, Houthi za ta ci gaba da kai harei kan jiragen ruwan Isra'ila

https://p.dw.com/p/4bEHp
Hoto: Mohammed Zaatari/AP/picture alliance

Sojojin Isra'ila sun kama wasu mata biyu 'yan uwan mataimakin shugaban kungiyar Hamas Saleh al-Arouri da Isra'ilar ta kashe a birnin Beirut na kasar Lebanon a farkon watan nan na Janairu.

Karin bayani:Kisan babban jami'in Hamas na ci gaba da samun martani

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito sojin Isra'ila na cewa sun kama matan ne bisa zargin furta kalaman tunzuri na aikata ta'addanci ga Isra'ila.

Kungiyar Hezbollah dai ta ce farmakin da Amurka da kawayenta suka kai kan 'yan Houthi na Yemen ba komai zai janyo ba, face haddasa rincabewar rikicin yankin, don haka babu gudu babu ja da baya, Houthi za ta ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra'ila da na aminanta a Baharmaliya.

Karin bayani:Hezbollah barazana ga fararen hula

Shugaban Hezbollah mai alaka da Houthi da ke samun goyon bayan Iran, Hassan Nasrallah, ya ce matakin Amurka da kawayenta zai kara rura wutar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, da ma gurgunta harkokin kasuwancin da ake gudanarwa ta jiragen ruwa da ke bi ta Baharmaliya.