Hakkin dan AdamHabasha
Amnesty ta zargi sojoji da yi wa mata fyade a Habasha
September 5, 2023Talla
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce sojojin kasar Iritiriya bisa hadin gwiwa da dakarun gwamnatin Habasha sun aikata munanan laifukan cin zarafin Bil Adama a yankin Tigray na Habasha.
Amnesty ta ce duk da tsagaita wuta da aka yi a yankin, sojojin Iritiriya na halaka fararen hula tare da yi wa mata fyade - karfi da yaji. Rahoto na musamman da kungiyar ta fitar a ranar Litinin ya ce dakarun Iritiriya na kuma kwasar wa jama'an yankin Tigray dukiya a matsayin ganima. Amnesty ta ce wadannan laifuka ne masu muni da aka aikata bayan sanya hannu a kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a yankin.