Saudiyya ta maida wa Alhazan Katsina kudadensu
May 24, 2018Maida kudin ga alhazan na Katsina kudaden Saudiyya ta yi na da nasaba da yadda kasar ta ga an take wasu hakkokin maniyatan duk kuwa da irin makudan kudaden da suka biya kafin su samu damar sauke faralin. Alh Muhammad Abu Rimi shi ne shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar ta Katsina ya kuma tabbatar da cewa kowanne Alhaji zai amshi kudaden daga cikin adadin da Saudiyya din ta maida wa jihar ta Katsina.
Tuni da hukumar jin dadin ta bayyana irin matsalolin da suka sanya aka wadanda suka hada da na gidaje batun sufuri. Baya ga matsalar wurin zama da alhazan suka fuskanta Alhaji Abu Rimi ya ce sun kuma fukanci matsalar cimaka da ya kamata a yi masu inda ya ce "akwai abubuwan da a can ya kamata a ce an yi wa Alhaji wanda kasar ta ce a yi masa amma ba su yi ba''.
Daya ba yan daya dai aka rika kiran alhazan na Katsina ana raba musu kudaden kuma tuni wanda suka karaba suka shaidawa wakilinmu na Katsina Yusuf Ibrahim Jargaba cewar komai ya tafi daidai. Rabi'u Sani Kurtufa guda ne daga cikin wanda suka karbi kudaden ya kuma ce ''an bani Naira dubu talatin da bagwai da dari biyar da Naira ashirin''.