1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyaran kundin tsarin mulki domin Touadera

Abdoulaye Mamane Amadou LMJ
August 8, 2023

Hukumomi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun ce da gagarumin rinjaye ne masu kada kuri'a a kasar suka aminta da sabon kundin tsarin mulkin da aka kada kuri'ar raba-gardama a kansa a makon jiya.

https://p.dw.com/p/4UuvI
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Bangui | Zabe |  Faustin Archange Touadera
Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Barbara Debout/AFP/Getty Images

Hukumomin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar dai sun bayyana hakan, duk da karancin masu kada kuri'ar da ganau suka ce an fuskanta a zaben da aka gudanar a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata. Hukumar Zaben Kasar mai Zaman Kanta ta nunar da cewa fiye da kaso 60 cikin 100 ne suka fito jefa kuri'ar, kana ta bayyana kaso fiye da 90 na masu kada kuri'ar sun amince da sabon kundin tsarin mulkin da ke shirin bai wa shugaba Faustin Archange Touadera damar ci gaba da jan zarensa a kan madafun iko. Masu adawa da Shugaba Touadera na ganin cewar matakin sauya kundin tsarin mulkin wata manufa ce na dawwama kan madafan iko, a manufarsa ta ci gaba da samun kariya daga dakarun sojojin hayar Wagner na kasar Rasha da ke kasar shekaru biyar kenan.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Bangui | Zaben Raba-gardama | Kundin Tsarin Mulki
Zaben Raba-gardama kan gyaran kundin tsarin mulki a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Barbara Debout/AFP/Getty Images

Sai dai ga dan majalisar dokokin jam'iyyun da ke kan karagar mulki Thimoléon Mbaïkoua batun ba haka yake ba, a cewarsa rinjayen kundin tsarin mulkin wani babban abin farin ciki ne. A yanzu dai ana dakon kotun tsarin mulkin kasar da ita za ta amince da sabon kundin tsarin mulkin, a ranar 27 ga wannan wata na Agusta da muke ciki. An sauya wa'adin mulkin daga shekaru biyar zuwa bakwai kana shugaban kasar ka iya tsayawa takara har iya sanda ya gaji domin radin kansa, lamarin da ake ganin ka iya bai wa shugaban kasar mai shekaru 66 damar yin tazarce a zaben kasar na shekarar 2025 da ke tafe. Wannan ba abin da zai haifar wa kasar face koma baya, in ji Me Crépin Mboli-Goumba da ke zaman guda daga cikin kawancen 'yan adawa. A cikin sabon kundin tsarin mulkin dai an bai wa shugaban kasa damar zabar mataimakinsa da kuma nada mambobin kotun tsarin mulki mafi rinjaye, kana an soke dokar da ke bayar da damar binciken duk wata yarjejeniyar da ta shafi hakar ma'adinai ga majalisar dokokin kasar.