1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin

Philipp Sandner | Mouhamadou Awal Balarabe AH/SB
July 28, 2023

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya za ta kada kuri'a kan sake fasalin tsarin mulki, wanda har yanzu ba su san abin da ya kunsa ba. Amma Shugaba Faustin Archange Touadéra zai ci gajiyar wannan sauyi sakamakon yunkurin tazarce.

https://p.dw.com/p/4UW5j
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya I Shugaba Faustin-Archange Touadéra
Shugaba Faustin-Archange Touadéra na Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Präsidentschaft der Republik Ruanda

Kuri'ar raba gadar za ta kasance kan makomar siyasar Shugaba Faustin Archange Touadéra  wanda ke kammala wa'adinsa na biyu kuma na karshe bisa ga dakokin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Amma gyaran kundin tsarin mulki da za a yi idan aka kada kuri'ar raba gardama za ta sake bashi damar sake tsayawa takara a zaben 2025. A hakikanin gaskiya ma dai, Touadéra mai shekaru 66 a yanzu zai iya rungumar salon mulkin sai Mahadi ka ture. Sai dai ministar harkokin wajen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Sylvie Baïpo-Temon ta ce al'umma ne ke da nauyin yanke alkiblar da kasar za ta dosa.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya I Masu zanga-zanga
Masu adawa da gyarar kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Jean-Fernand Koena/DW

Fadar mulki ta Bangui ta ce irin wannan hanya ne kasashen Amirka da Faransa a ko yaushe suke amfani don iyakance wa'adin shugabanninsu.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ya fama da yake-yaken basasa da dama a cikin shekarun da suka gabata. Amma kuma a kokarin maida kasar kan tsarin dimokuradiyya, tsarin mulki da ake amfani da shi a yanzu ya fara aiki a shekara ta 2016, gabanin fara wa'adin mulkin shugaba Touadéra na farko. Amma babban Bishop na Bangui babban birnin kasar Dieudonné Nzapalaïnga, ya ce yunkurin da ya kai ga samar da kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi ya sha bamban da na yanzu.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya I Masu goyon bayan sauya kundin tsarin mulki
Masu goyon bayan sauya kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Barbara Debout/AFP/Getty Images

Sai dai a yanzu babu alamar wannan yanayi na kyakkyawar zamantakewar siyasa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Maimakon haka ma, yunkurin kwaskware kundin tsarin mulkin ya gudana ne tsakanin wasu tsirarun kananan kungiyoyi ba tare da yada ayyukansu ga jama'a ba. Sannan jinkiri da hukumar zabe ta yi wajen fitar da cikakken daftarin sabon kundin tsarin mulkin ya sa muhawara ta raja'a ne kan yunkurin tazarce na shugaban da ke kan karagar mulki. Amma Samson Itodo, lauyan Najeriya da ya kware kan harkokin dimokuradiyya a Afirka, ya ce aikin tsarin mulki na yanzu ba shi da alaka da ainihin dalilan sake fasalin kundin tsarin mulkin.

Watanni biyu da suka wuce ne aka sanar da jadawalin zaben raba gardamar, amma kuma a fayyace duk abubuwan da daftarin ya kunsa ba. A daya hannun kuma ba a yi rajistar masu zabe ba, saboda haka 'yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na iya gabatar da duk wata takarddar shaida don tantancewa, lamarin da ya yi hannun riga da tsarin kasar. Uwa-uba kuma ba a tabbatar da tsaro a wasu sassa na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba.