1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɗan ta'adar Norway ya sake kai ziyara a tsibirin Utoya

August 14, 2011

'Yan sanda sun ɗauki Breivik zuwa tsibirin na Utoya ne a matsayin yanki na biciken da ake gudanarwa akan mutuwar mutane 68

https://p.dw.com/p/12GQ9
Ɗan ta'adar Norway Anders BrevikHoto: picture alliance/dpa

Anders Behring Breivik da ake tuhuma bisa laifin aikata ta'addanci a ƙasar Norway a yau ya sake kai ziyara a tsibirin da ya hallaka mutane 68 amma ba tare da nuna nadama ba. Breivik wanda ake tsare da shi tun ranar 25 ga watan da ya gabata ya amsa laifin ta da bom daga cikin mota da yayi sanadiyar mutuwar mutane takwas a birnin Oslo da kuma harbe harbe a tsibirin Utoya. 'Yan sanda sun ɗauki Breivik zuwa tsibirin na Utoya ne a matsayin yanki na biciken da ake gudanarwa akan mutuwar mutane 68 da suka gamu da ajalinsu a lokacin da suke halartar taron reshen matasa na jam'iyyar Labour da ke mulkin ƙasar ta Norway. An ɗauki Breivik zuwa tsibirin na Utoya ne a daidai lokacin da jam'iyyun siyasa ke ƙaddamar da kamfensu na zaɓukan ƙananan hukumoni da jihohi da za su gudana a wata mai zuwa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala