Ƙungiyar ISIL ta ƙwace iko da ƙarin wasu yankuna a Iraƙi
June 13, 2014Talla
Rahotannin sun kuma ce yanzu haha 'yan tawayen na ƙoƙarin ƙara danawa zuwa birnin Bagadaza. Masu aiko da labarai sun ce masu kishin addinin galibi 'yan sunni da ke fafutukar kafa daula Islama a Iraƙin,a jiya suna daf da ratan kilomita 90 misali awa ɗaya daga Bagadaza bayan da suka ƙwace iko da garin Duhuliya.
Yanzu haka biranen Mossul da Tikirit sun faɗa cikin hannu 'yan tawayen tun ran Larba. Shugaban Amirka Barack Obama ya ce suna ƙoƙarin samar da hanyoyin taimaka wa Iraƙi.
'' Ina ganin yin haka dai dai nan gaba a lokacin wata tattaunawa da za mu yi da hukumomin Iraƙin za mu ganin irin taimakon da za mu ba su.''
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu