Ƙungiyar AU ta ɗage taronta daga Malawi
June 12, 2012Talla
Ƙungiyar Tarayyar Afrika, wato AU ta dage zaman taronta da zata gudanarwa a nan gaba a cikin watan Yuli mai zuwa daga ƙasar Malawi ya zuwa kasar Habasha wato a birnin Adis Ababa.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne tun bayan da kasar ta Malawi ta ɗauki alƙawarin cafke shugaban ƙasar Sudan Omar Hassan Al Bashir da zaran ya jefa kafa a ƙasar domin ta mutunta sammacin da kotun kasa da kasa ta ICC ta bada a kan shi tun a shekara ta 2009.
Ministan harakokin wajen kasar ta Sudan ya ce wannan wata alama ce da ke tabbatar da irin nasarorin da suke samu a duniya bisa ga makarkeshiyar kotun ta ICC.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi