Zuma na zargin kasashe makwabta da rura wutar kyamar baki.
April 27, 2015Talla
A cikin wani jawabi da ya gabatar albarkacin samun 'yancin kan kasar Shugaba Zuma ya zargi kasashen Afrika musamman makwabtan kasar tasa da taimakawa wajan yaduwar wanann matsala ta kyamar baki a Afirka ta Kudu, yana mai zargin bakin da kin zama a kasashensu na asali. Shugaba Zuma ya ce wannan batu ne da ya kamata a tattauna a kansa a taron kungiyar kasashen kudancin Afirka ta SADEC dama na kungiyar Tarayyar Afrika AU, a cewarsa 'yan kasashen Afirka da ke kasarsa da dama ne suka bayyana dalillansu na zuwa Afirka ta Kudu da rashin gamsuwa da yanda shugabannin ksashensu ke tafiyar da mulki.