Ziyarar wurin faduwar jirgin Germanwings
March 31, 2015Manyan jami'ai daga kamfanin da ke lura da harkokin sufurin jiragen sama na Luhfthansa da Germanwings a gobe Laraba zasu ziyarci yankin tsaunika da ake wasannin zamiyar kankara a Faransa inda jirgin saman Germanwings ya fadi tare da hallaka mutane da dama a makon da ya gabata.
Carsten Spohr jagoran kamfanin Lufthansa da Thomas Winkelmann na Germanwings zasu ziyarci yankin na Seyne-les-Alpes da safiyar ta gobe Laraba inda zasu ga yadda jami'ai ke aikin ceto tare da yin addu'oin ban kwana ga mutane 150 da suka rasa rayukansu a lokacin wannan mummunan hadari faduwar jirgin saman.
A ranar Talatannan ma dai shugaba Francois Holland ya bayyana cewa nan ba da dadewa bane za a gano wadanda bala'in faduwar jirgin ya ritsa da su a daidai lokacin da kamfanonin inshora suka ware daruruwan miliyoyin dalar Amirka dan biyar diyya ga iyalan mamatan.