1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudus: Ziyarar ministan tsaron Isra'ila

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
January 3, 2023

Ziyara sabon ministan tsaron Isra'ila mai matsanancin ra'ayin kishin addini Itamar Ben-Gvir a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke birbnin Kudus, wurin da Musulmi da Yahudawa ke girmamawa ta janyo cece-kuce.

https://p.dw.com/p/4Lhah
Isra'ila | Ministan Tsaro | Itamar Ben-Gvir | Ziyara | Kudus | Al-Aqsa
Ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben-GvirHoto: Abir Sultan/AP/picture alliance

Ziyarar ta sabon ministan tsaron Isra'ilan dai, ta samu martanin suka daga bangarori da dama. A lokacin da yake tafiya cikin harabar masallacin da ke birnin Kudus Itamar Ben-Gvir ya ce, wannan wurin a bude yake ga kowa da kowa har ma Yahudawa. Hotunan faifan bidiyo sun nuna shi yana yawo a gefen harabar ginin masallacin, tare da wasu manyan jami'an tsaro da kuma wani Bayahude mai ra'ayin mazan jiya a gefensa. Ko da yake ziyarar ta wuce ba tare da wata matsala ba, tana iya haifar da barazanar rikici a bangaren Falasdinawan da tuni suka fuskanci tashe-tashen hankula a yankunan Yahudawa da suka mamaye Gabar Yamma da Kogin Jordan a shekarar da ta gabata. Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh dai, ya yi kira ga al'ummarsa da su nuna adawa da samamen da aka kai Masallacin Al-Aqsa.

Masallaci | Al-Aqsa | Kudus | Musulmi | Yahudawa
Masallacin Al-Aqsa dai, na da matukar muhimmanci ga Musulmi da YahudawaHoto: Ammar Awad/REUTERS

Ben-Gvir ya taba bayar da shawarar kawo karshen hana Yahudawa yin aikin ibada a wurin, amma ya nuna bai damu da batun sosai ba tun lokacin da ya hada kai da Netanyahu. Sai dai har yanzu sauran mambobin jam'iyyarsa, suna ba da shawarar daukar wannan mataki. Kasancewar Ben-Gvir da ke zaman guda daya daga cikin masu matsanancin ra'ayin rikau a tarihin Isra'ila cikin gwamnatin Benjamin Netanyahu ya kara zafafa fushin Falasdinawa, kan kokarinsu na tabbatar da 'yantacciyar kasar Falasdinu. Netanyahu wanda yanzu ke kan wa'adinsa na shida a matsayin firaminista ya yi alkawarin karfafa zaman lafiya a yankin da kuma kokarin cimma sababbin yarjejeniyoyi. Ben-Gvir dai shi ke kula da 'yan sandan Isra'ila, wadanda ke da alhakin aiwatar da dokar hana Yahudawa yin ibada a harabar masallacin. Isra'ila tana daukar birnin Kudus a matsayin babban birninta, duk da cewar ba a amince da hakan a matakin kasa da kasa ba. A nasu bangaren Falasdinawa na son gabashin Kudus da ginin masallacin yake, a matsayin babban birnin wata kasa da suke fatan tabbatarwa a nan gaba.