Ziyarar Barack Obama a Afirka
June 28, 2013Ziyarar shugaban Amirka Barack Obama a Afirka ta fi daukar hankalin jaridun na Jamus a wannan mako. A lokacin da take tsokaci a kan ziyarar jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi.
"Mutane da yawa sun ji takaicin yadda aka dauki lokacin mai tsawo kafin shugaban Amirka ya kai ziyara Afirka. Amma ganin cewa yanzu ya sake kai ziyara wannan nahiya, hakan na da alaka da angizon da kasar China ke kara samu a nahiyar. Tun gabanin ziyarar, mataimakin mai ba wa Obama shawara kan harkokin tsaro Ben Rhodes ya ce Amirka na da muradi mai girma a Afirka kuma nahiyar wani yanki ne da Amirka za ta karfafa ayyukanta a cikin shekaru masu zuwa. Idan aka dubi tawagar dake dafa wa Obama baya za a kara fahimtar wannan magana. Tawagar dai ta kunshi daruruwan manyan 'yan kasuwar Amirka dake yi wa shugaban rakiya domin kyautata dangantakar kasuwancinsu da Afirka, da suka yi sake har ta kubce musu. A halin yanzu dai kasashe bakwai daga cikin kasashe 10 dake samun bunkasar tattalin arziki cikin sauri a Afirka suke, kuma tuni ake rige-rigen neman dinbim albarkatun wannan nahiya, karkashin jagorancin kasar China."
Rangadi mai muhimmanci ga Afirka
Rangadin Obama a Afirka inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai cewa shugaban na Amirka na wata ziyara mai muhimmanci a wasu kasashen Afirka da suka hada da Senegal da Afirka ta Kudu da kuma Tanzaniya.
"Wadannan kasashe uku da Obama ya zaba, manyan amiman Amirka ne wadanda kuma ke tafiyar da kyakkyawan mulkin demokradiyya. Obama ya yi wa Kenya, kasar da mahaifinsa ya fito, dan-wake zagaye domin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasar a watan Maris wato Uhuru Kenyatta, kotun duniya mai hukunta manyan laifukn yaki tana neman sa bisa zargin hannunsa a mummunan rikicin da ya biyo bayan zaben kasar na shekarar 2007. Kawo yanzu Afirka ba ta a jerin farko a kan ajandar shugaban na Amirka duk da cewa bayan zaben Obama karon farko a matsayin shugaban Amirka nahiyar ta yi babban fatan kyautata dangantaka ta kut da kut da Amirka. Amma magabatansa George W Bush da Bill Clinton sun fi nuna sha'awa ga nahiyar wadda suka kai wa ziyara a lokuta da dama."
Karancin shaddodin zamani a Afirka ta Kudu
'Yan Afirka ta Kudu sun fusata game da rashin isassun wuraren ba haya inji jaridar Neues Deutschland sannan sai ta ci gaba kamar haka.
"Daga cikin abubuwan da muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya akwai batun rage yawan mutanen da ba sa samun wuraren ba-haya mai tsabta da kashi 50 cikin 100 daga shekarar 1990 zuwa 2015. Amma duk kokarin da kasashe ciki har da Afirka ta Kudu suka yi kawo yanzu bai kai ga cimma manufa ba. Don nuna fushinsu ga hukumomi a kwanankin nan mazauna lardin yammacin Cape dake zama na biyu mafi girma a Afirka ta Kudu, sun yi jifar ayarin motocin Firimiyar lardin da ba-haya lokacin da ta kai ziyara unguwar Khayelitsha don wayar da kai a kan batun kare muhalli. Mutane na zarginta da rashin samar da wuraren ba-haya masu tsabta. Unguwar da mafi yawan mazauna ciki talakawa ne na daya daga cikin unguwannin marasa galihu a kasar ta Afirka ta Kudu dake fama da yaduwar cututtuka masu nasaba da rashin tsabtar muhalli."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu