Zargi na yawaita kan Faransa game da Haftar
April 19, 2019Talla
Ma'aikatar cikin gidan Libiya ta sanar da dakatar da harkokin diplomasiyya tsakaninta da Faransa jim kadan bayan bayyana takaici game da rawar da Faransa take tawaka a rikicin da ya hana Libiya zama lafiya. Sai dai ana ta bangaren Faransa ta kara jaddada amincewa da gwamnatin Firaminista Fayed al-Sarraj a matsayin jogora a Libiyan da kuma matakin sulhunta bangarorin da suka hana warware rikicin siyasar kasar da Majalisar Dinkin Duniya take yi a yanzu.
A wani sabon labarin kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa cikin wannan wata na Afirilu mutane 205 ne suka rasa ransu a Libiya sakamakon rikicin bangarorin da ke yaki da juna lamarin da ya sanya ta tura kwararru a harkar lafiya don yi wa wadanda suka jikkata magani