1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zanga-zanga ranar bikin 'yanci

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 1, 2024

A daidai lokacin da Najeriya ke bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin cin gashin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, al'ummar kasar sun bazu a kan tituna domin yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

https://p.dw.com/p/4lIG1
Najeriya | 'Yanci | Zanga-zanga
Matasa na zanga-zanga a ranar cika shekaru 64 da samun 'yancin NajeriyaHoto: Leonid Altman/Zoonar/picture alliance

A jihohi da dama na Najeriyar, dandazon masu zanga-zangar a karo na biyu cikin watanni biyu sun fito dauke da kwalaye da kuma tutocin kasar tare da neman samun damarmaki da ayyukan yi ga matasa a kasar da ke zaman mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka. A yanzu haka dai Najeriyar na zaman guda daga cikin kasashen duniya masu fama da fatara da yunwa, duk da kasancewar ta cikin kasashen duniya masu arzikin man fetur.