Boren kin jinin dokar zama dan kasa ta kankama a Indiya
December 19, 2019Talla
Masu bore da zanga-zanga sun yi dauki ba dadi da jami'an tsaro wasu sassan kasar da dama musamman ma a birnin New Delhi da sauran jihohin da ke arewacin kasar, kana tuni jihohin suka kirkoro dokokin da ke hana duk wani taro na jama'a da suka wuce mutun hudu. Tuni hukumomin kasar suka dauki matakin toshe duk wasu kafafe na sadarwa irin na zamani a yankunan da ake fama da zanga-zangar ciki har da wasu wurare a birnin Delh. Masu aiko da rahotanni sun ce an hallaka mutane da dama a yayin zanga zangar wacce ta doshe mako daya.