Touadera ya yi alkawarin hada kan yan kasa
January 5, 2021Talla
Da kuri'u kashi 53.9 ne shugaban mai shekaru 63 ya sake nasara a cewar hukumar zaben kasar ANE, sai dai a makon da ya gabata 'yan adawa sun bukaci soke zaben da suka kira mai cike da magudi.
A ranar Lahadin ta shige, 'yan tawaye sun karbe iko da birnin Bangassou mai tazanar kilomita 750 daga gabashin Bangui babban birnin kasar, a ranar Litinin kuma babban mai gabatar da kara na gwamnati ya kaddamar da bincike kan tsohon shugaban kasar Francois Bozize, kan zargin yunkurin kifar da gwamnati gabanin zabe.