1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a sanya sunayen 'yan takarar Jam'iyyar APC a Zamfara

Ramatu Garba Baba
February 22, 2019

Hukumar zabe me zaman kanta ta kasa a Najeriya wato INEC, ta yanke hukuncin sanya sunayen 'yan takarar Jam'iyyar APC a jihar Zamfara dan shiga zaben da zai gudana a gobe Asabar.

https://p.dw.com/p/3DtxO
Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Matakin ya biyo bayan hukuncin wata babbar kotu da ke Abuja da ta umarci INEC kan ta karbi sunayen. Amma rahotanni sun nuna har yanzu ta na kasa ta na dabo, domin babu tabbacin INEC za ta sanya sunayen 'yan takarar gwamnan jihar.  Akwai hasashen yiwuwar a sa wasu daga cikin masu adawa da gwamnatin jihar da ake kira G8. Yanzu dai ana jira a ji sunayen 'yan takarar da uwar jam'iyyar APC ta kasa ta bai wa hukumar zaben.