1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa gabannin zabe a Zambiya

Abdul-raheem Hassan
August 7, 2021

Shugaban jam'iyyar adawa a kasar Zambiya ya ce an hana shi zuwa gangamin yakin neman zabe a tsakiyar lardin Copperbelt, matakin da ya ce zai iya yin katsalandan a zaben mako mai zuwa.

https://p.dw.com/p/3yh3X
Sambia Lusaka Wahlen Präsidentschaftskandidat Hakainde Hichilema
Hoto: Getty Images/AFP/G. Guercia

Kasar Zambiya mai arzikin tagulla za ta shiga zabe a wani fafatawa mai karfi tsakanin tsoffin abokan hamayya, tsohon dan adawa Hakainde Hichilema da Shugaba Edgar Lungu. Shi dai dan adawa Hichilema, wani hamshakin dan kasuwa ne mai shekaru 59 wanda ke neman takara karo na shida.

 Jagoran adawar kasar Hichilema ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "An hana ni zuwa Copperbelt saboda Mista Lungu yana can" a cewar jam'iyyar adawa United Party for National Development (UPND) wannan ba hujja ba ne na hana shi zuwa shi ma yakin neman zabe.