1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman taron hukumar CESOC a Nijar

Gazali Abdou TessaouaSeptember 18, 2014

Hukumar CESOC wacce ke baiwa gwamnatin ta Nijar shawarwari a fannin tattalin arziki, zamantakewar alumma da al'adu, ta bude zaman taronta na shekara karo na biyu.

https://p.dw.com/p/1DFJO
Hoto: DW/M. Kanta

A wanan zama hukumar za ta tattauna akan jerin wasu matsaloli da ke addabar kasar ta Niger, musamman dangane da fannin tsaro, da noma da kiwo, da batun kishin kasa, da dai sauran matsaloli da ke yin barazana ga cigaba, dama zaman lafiyar alummar kasar.

Wakillai sama da dari ne wadanda su ka fito daga jihohi 8 na kasar ta Nijar ne su ke halartar wannan taro na hukumar ta CESOC wanda a wanann karo ma, zai tattauna akan jerin wasu matsaloli da ke addabar kasar ta Niger domin gabatar wa gwamnati. Ita dai wannan hukumar na ganin cewa, yan Niger da dama na da rauni wajan abun da ya shafi batun kishin kasa, wanda kuma ta ce shine tushen duk wani koma baya da kasar ke fuskanta.

Flüchtlingsfamilie aus Nigeria bei Diffa Niger
Hoto: DW/Larwana Malam Hami

Sai dai a daidai lokacin da wasu ke korafi akan matsalolin kishin kasa, da batun kiwo da na noma, shi kuma daga nashi bengare Alhaji Bulama Isa wakilin jihar Diffa a wurin wannan taro, tsokaci ya yi akan matsalar kwararowar yan gudun hijira daga Tarayyar Najeriya, dama barazanar yan kungiyar Boko Haram a yankin gabacin kasar ta Nijar ganin yadda jihar da Diffa ke makwabtaka da jihar Borno. Kimanin kwanaki 20 ne dai, hukumar ta CESOC za ta share tana gudanar da wannan taro nata inda ake sa ran daga karshe za ta fito da shwarwari akan matsalolin da ta tattauna akansu domin gabatarwa gwamnati.