Zage damtse wajen yakar Ebola
September 13, 2014Talla
Ma'aikatar lafiya ta kasar Kyuba ta ce za ta tura sama da jami'an kiwon lafiya 160 zuwa kasar Saliyo domin taimakawa a kokarin da ake na kawo karshen cutar Ebola mai saurin kisa da ta bulla a yankin yammacin Afirka. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yaba da wannan yunkuri inda ta ce za su taimaka gaya, sai dai ta ce ana bukatar kimanin jami'an kiwon lafiya 1,500 ne domin kula da wadanda suka kamu da cutar ta Ebola a kasashen yammacin Afirkan. Kiyasin hukumar ta WHO dai ya nunar da cewa akallah rayukan mutane 2,400 ne cutar ta lakume a kasashe hudu da ta bulla da suka hadar da Laberiya da Gini da Saliyo da kuma Najeriya.