1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Saliyo a yau asabar

September 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuC8

A yau asabar a kasar Saliyo ake gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. Shugaban ´yan adawa Ernest Koroma ke fafatawa da Solomon Berewa dan takarar jam´iyar da ke jan ragamar mulkin kasar a yanzu. Masu sa ido a zabe sun ce bisa ga dukkan alamu za´a sha da kyar kafin a sakamakon zaben. A zagayen farko na zabern babu daya daga cikin ´yan takara da ya samu yawan kuri´u na kashi 55 cikin 100 da ake bukata don darewa kan kujerar shugaban kasa. Kuri´ar na matsayin zakaran gwajin dafi na jaririyar demukiradiyya a kasar ta Saliyo wadda ta yi fama da yakin basasa.