1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Zabtarewar kasa ta kashe mutane 14

Abdul-raheem Hassan
June 30, 2022

Akalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu, wasu fiye da 30 suka bace bayan zabtarewar laka sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya a arewa maso gabashin Indiya .

https://p.dw.com/p/4DUQg
Bildergalerie | Schwere Überflutungen in Indien und Bangladesch
Hoto: Anuwar Hazarika/REUTERS

Ma'aikatan bayar da agajin gaggawa yayin afkuwar bala'o'i da 'yan sanda da mazauna kauyen na kokarin ceto wadanda ke binne a karkashin kasa, a wani gari kusa da Imphal babban birnin jihar Manipur.

Hukumomi sun bayyana cewa zabtarewar lakar ta lalata layukan dogo tare da haddasa barna mai yawa da zuwa yanzu ba a tantance adadinta ba.