Bala'i
Aikin ceto bayan zabtarewar kasa
December 16, 2022Talla
Kimanin mutane takwas ne rahotanni ke cewa sun mutu da sanyin wannan safiya wannan Jumma'a a tsibirin Genting na kasar Malesiya, sakamakon iftila'in zaftarewar kasa. Bayanai na cewa akwai ma wasu sama da mutum 50 da suka bace bayan faruwar lamarin a wani yanki da ke samun bakuncin masu yawon shakatawa.
Kimainin mutane 80 ke a wajen lokacin da ibtila'in ya faru, kuma jami'ai na cewa an yi nasarar ceto mutane 23 kawo yanzu.
Tsibirin Genting dai na cikin gundumar Selnagor da ke da karfin arziki a Malesiya, kuma a baya ya sha fama da bala'in zaftarewar kasar. Tsibiri da ke da kyawun gaske ga mutane daga sassa daban-daban na duniya na zuwa ziyarar kashe kwarkwatar ido.