Zaben yanki a birnin Berlin na Jamus
September 18, 2016Masu kada kuri'a a birnin Berlin na nan Jamus sun fita a ranar Lahadin nan dan zaben yanki zaben da jam'iyyar masu adawa da baki ta AfD ke fatan za ta ci gaba da amfani da fushin tsirarun Jamusawa da ke adawa da tsarin Shugaba Merkel kan 'yan gudun hijira.
Samun sabbin magoya baya dai ga jam'iyyar masu adawa da baki musamman a birnin na Berlin da ke da gambiza ta al'umma da ke nuna ta na da kashi 14 cikin dari na magoya baya na zama babban kalubale ga Shugaba Merkel da ta ga nuna adawa kiri-kiri a yayin zanga-zanga a wannan mako, sannan a bangare guda ke da shekara gaba kafin zaben gama gari.
Jam'iyyar ta CDU dai na da magoya baya a fadin kasar yayin da a bangaren na birnin Berlin SPD karamar kawa ga CDU ke da karfi, sai dai magajin garin na Berlin Michael Mueller na SPD ya ce a wannan karo kawancen da Merkel ba da su ba.