Zaben shugaban kasa a Gabon mai arzikin man fetir
November 27, 2005Talla
A kasar Gabon ma a yau lahadi ake gudanar da zaben shugaban kasa, inda bisa ga dukkan alamu shugaba mai ci Omar Bongo zai lashe wannan zabe. Tun a shekarar 1967 shugaban mai shekaru 69 da haihuwa ya ke shugabantar kasar ta Gabon. Yanzu haka dai shine shugaban Afirka mafi dadewa akan karagar mulki. ´Yan adawa da suka yi zargin tabka magudi a zaben da aka yi a baya, a yanzu ma suna korafin cewa shugaban Bongo zai yi aringizo kuri´u don yayi tazarce a kan kujerar shugaban kasar mai arzikin man fetir.