1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Bavaria mai tasiri a siyasar Jamus

Yusuf Bala Nayaya
October 14, 2018

Fiye da mutane milyan tara da dubu dari hudu ne suka cancanci kada kuri'a a zaben yanki a Jihar Bavaria anan Jamus wannan Lahadi, zaben da ake ganin zai yi tasiri ga makomar jam'iyyar kawancen shugabar gwamnatin Jamus.

https://p.dw.com/p/36Vlq
Landtagswahl in Bayern Horst Seehofer 15.09.2013
Hoto: Getty Images

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a a wannan mako dai ta nunar cewa jam'iyyar 'yan ra'ayin mazan jiyan ta CSU na da tsakanin kashi 33 zuwa 34 cikin dari na masu goyon baya, yayin da jam'iyyar 'yan fafutikar kare muhalli ta Green ke zama ta biyu da kashi 18 cikin dari.

Jam'iyyar ta CSU daga jihar ta Bavaria dai ta kasance babbar kawa a gwamnatin da CDU ke jagoranta karkashin Angela Merkel inda ma jagoran jam'iyyar Horst Seehofer ke zama ministan harkokin cikin gidan Jamus.

Merkel dai ta ki cewa komai game da ko zaben zai tasiri a gwamnatin kawancensu da CSU? Sai dai ta ce jam'iyyar "na fiskantar yanayi mara dadi" tana mata fatan nasara a zaben. Da karfe shida na yamma za a rufe tashohin kada kuri'a kana a fara nuna hasashen sakamako na farko a kafafen yada labarai na kasa a Jamus.