Zaben Gabon
December 18, 2006Talla
A kasar gabon gamaiyar jamiyu dake goyon bayan shugfaba Omar Bongo shugaban kasa mafi dadewa a Afrika,itake kann gaba a zaben yan majalisa da aka gudanar a kasar.
Duk da cewa a gobe ne ake sa ran samun cikakken sakamakon zaben na ranar lahadi,amma rahotanni daga birnin Libraville babban birnin kasar sun nuna cewa gamaiyar jamiyun ta Omar Bongo ke kann gaba.
Ana sa ran wannan zabe zai sake baiwa Bongo damar ci gaba da mulkin kasar wanda yayi shekaru 40 yanayi.
A kuma 1967 Omar Bongo ya karbi ragamarv mulkin kasar mai arzikin man fetur wadda kuam ke fama da talauci da rashin aikin yi.