1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Gabon ya bar baya da kura

Latheefa Mustapha Ja'afar/A'RaheemAugust 29, 2016

Al'ummar kasar Gabon na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da suka gudanar a karshen mako. Sai dai al'ummar na dakon ne cikin fargabar yi wuwar sake barkewar rikicin bayan zabe.

https://p.dw.com/p/1Jrsa
Bildkombo Ali Bongo und Jean Ping Gabon
Hoto: picture-alliance/dpa/E.Laurent/L.JinMan

Kwana guda kafin a bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a hukumance, tuni dai dan takarar jam'iyyar adawa a zaben shugaban kasar da aka gudanar a Gabon Jean Ping ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben na karshen mako, inda bangaren jam'iyyar adawar ta Ping suka ce su ke da kaso 60 cikin 100 na kuri'un da aka rigaya aka kidaya, koda yake babu wani tabbaci kan ikirarin nasu.

Shugaban aksar Gabon, Ali Bango Ondimba
Shugaban kasar Gabon, Ali Bango OndimbaHoto: AP

Tuni dai bangaren shugaban kasar mai ci wanda shi ma ya tsaya takarar shugabancin kasar ta Gabon a zaben na bana Ali Bongo ya bayyana batun na Ping a matsayin mai hadari ga zaman lafiyar kasar.

Ping ya bayyana samun nasarar ne gabanin bayyana cikakken sakamakon a ranar Talata inda ya ce:

"Babu wata bita da kuli, zan kasance shugaban dukkanin 'yan Gabon."

To sai dai Alain Claude Bilie By Nzé da ke zaman kakakin shugaban kasar Gabon kuma abokin takarar Ping a zaben na karshen mako wato Shugaba Ali Bango bangaren da su ma suka ayyana samun nasara sun ce:

"Za mu iya tabbatar da cewar dan takararmu Ali Bango Ondimba ya samu nasara, muna kan hanyar yin wa'adin mulki na biyu."

madugun adawa a kasar Gabon, Jean Ping
Madugun adawa a Gabon, Jean PingHoto: Reuters/E. W. Obangome

Rahotanni dai sun nunar da cewa zaben Gabon a bana ya tafi cikin kwanciyar hankali ba tare da tayar da zaune tsaye ba. Sai dai masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai a zaben na Gabon sun soki lamirin zaben wanda suka ce akwai alamun magudi a cikinsa. A tun shekara ta 2009 ne dai shugaba Ali Bongo mai shekaru 57 a duniya ke mulkin kasar ta Gabon tun bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo da ya shafe shekaru 41 yana mulkin kasar. Al'ummar kasar dai na cikin fargabar sake barkewar rikici makamancin wanda ya afku a shekara ta 2009 bayan da aka ayyana Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar kana.