Zaben Afirka ta Kudu ya dauki hankalin Jaridun Jamus
June 2, 2024Jaridar Die Zeit cikin sharhinta mai taken: "Sun aikata mummunan kudirinsu cikin dare." A Ruwanda dan jarida mai binciken kwakwaf ya mutu cikin wani yanayi na diga ayar tambaya. Shin wannan kasar za ta iya zama abokiyar hulda ga kasashen Turai? Jaridar ta ce abin da yake da tabbas shi ne, za a fahimci cewa dan jaridar mai binciken kwakwaf na Ruwanda John Williams Ntwali yana cikin firgici. Abin yana damunsa, a yininsa na karshe da yake zaune tare da abokinsa a Kigali a watan Janairun 2023. Mai shekaru 43 a duniya a wannan lokacin, Ntwali yana da kafar yada labarai da yake watsawa a tashar YouTube mai suna PAX TV – Ireme News da kimanin mutane dubu 42 ke bibiya. Dan jaridar ya yi imanin cewa: Jami'an tsaron farin kaya na gwamnatin Ruwanda na bibiyarsa saboda yanayin aikinsa. Wannan shi ne bayanan irin tsoron da ya rinka bayyanawa wadanda suka yi tattaunawar sirri da shi a karshen rayuwarsa a Kigali babban birnin Ruwandan da ma ta wayar tarho.
Ita kuwa jaridar ZEIT ONLINE ta rubuta nata sharhin ne mai taken: Sansanin sojojin Jamus ya ci gaba da kasancewa a bude, duk da janye dakarun hadakar EU daga Nijar. A karshen watan Yuni sojojin na kungiyar Tarayyar Turai za su kawo karshen aikinsu a Jamhuriyar Nijar. Sai dai duk da haka gwamnatin Jamus na son sansanin sojojinta na Bundeswehr, ya ci gaba da kasancewa. Jaridar ta ce: Bayan sanar da kawo karshen aikin sojojin Tarayyar Turai EU, Jamus za ta kyale bangaren sufuri na sojojinta a Nijar. Jamus din da Jamhuriyar Nijar sun cimma matsaya ta wucin-gadi, na ci gaba da kasancewar rundunar ta Bundeswehr a Nijar kamar yadda ma'aikatar harkokin tsaron Berlin din ta sanar.
Burkina Faso ta koma karkashin mulkin kama-karya da sabon tsarin gwamnatin rikon kwarya, jagoran gwamnatin mulkin soja Ibrahim Traoré ya karawa kansa wa'adin mulki har zuwa 2029 in ji jaridar die tageszeitung. Suma sojojin da suka kifar da gwamnati a kasashen Mali da Nijar da kuma Guinea, sun kara nasu wa'adin mulkin. Jaridar ta ce sojojin da suka kifar da gwamnati a Burkina Faso, za su jima a kan mulki. Shugaban gwamnatin mulkin sojan Ibrahim Traoré ya sanya hannu kan wata sabuwar dokar gwamnatin rikon kwarya, wacce daga ranar biyu ga watan Yulin wannan shekarar za ta ba shi damar kai wa shekara ta 2029 yana kan karagar mulki. A watan Satumbar shekara ta 2022 ne dai, mai shekaru 36 a duniya Traoré ya kifar da gwamnatin dimukuradiyya a kasar da ke yankin Sahel. Burkina Faso dai na fama da matsalar yakin basasa, tsakanin sojojin gwamnati da kuma na masu tsattsauran kishin addini da ke ikirarin jihadi da ya yi sanadiyyar rayukan kimanin mutane dubu 20 yayin da wasu miliyan biyu suka kaurace wa gidajensu.
Ba mu karkare da jaridar Der Tagesspiegel da ta rubuta nata sharhin mai taken: "Zaben Afirka ta Kudu: Ko karshen mulkin jam'iyya guda ya zo? Akwai yiwuwar babban zaben Afirka ta Kudu ya kafa tarihi, hasashe ya nunar da cewa jam'iyyar ANC mai mulki ka iya rasa rinjaye a karon farko tare da dogaro a kan kafa gwamnatin hadaka." Jaridar ta ce wannan ka iya kawo karshen mulkin jam'iyya daya a kasar, wadda ta kwashe tsawon shekaru tana mulki tun bayan komawarta kan tafarkin dimukuradiyya a shekara ta 1994. Tun daga wancan lokaci, jam'iyyar ANC ta marigayi dan gwagwarmayar yaki da mulkin wariyar launin fata Nelson Mandela ke kan madafun iko a Afirka ta Kudu. Bayan tsawon shekaru 30, mutane da dama ba sa goyon bayan mulkin dimukuradiyya a kasar kasancewar ba sa amfana da tsare-tsaren gwamnati. Wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar, na nuni da cewa Afirka ta Kudu ta fi kowacce kasa nuna rashin daidaito a tsaknin al'umma. Kasar na kuma cikin na kan gaba, a batun rashin aikin yi a tsakanin matasa.))