1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a zabi sabon shugaban kasa a Somaliya

June 29, 2021

A wani mataki na kawo karshen takaddamar siyasa a kasar, masu ruwa da tsaki a Somaliya sun yanke shawarar zaben sabon shugaban kasa daga cikin 'yan majalissar kasar.

https://p.dw.com/p/3vmXA
Somalia Mogadischu Premierminister Mohamed Hussein Roble
Hoto: Sadak Mohamed/AA/picture alliance

Firaministan na Somaliya Mohamed Hussein Roble ya shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar na SONNA cewa, biyo bayan wata doguwar tattauna wa tsakanin kwamitin dattawan kasar da jam'iya mai mulki, dattawan zasu zabi 'yan majalisar da zasu zabi sabon shugaban a ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa.

Tun da fari dai hukumar zaben kasar ta bayyana cewa ba za ta iya gudanar da zabe ba sakamakon kalubalen tsaro da ake fama da shi, wanda ya baiwa kwamitin dattawa damar zaben masu zaben shugaba a Somaliya shekaru da dama da suka gabata.