Za a yi zaɓen majalisa a cikin watan Nuwamba a ƙasar Holland.
July 2, 2006Talla
Ƙasar Holland, ta ba da sanarwar gudanar da zaɓen majalisar dokoki a cikin watan Nuwamba mai zuwa. Hakan dai ya zo ne bayan murabus ɗin da Firamiyan ƙasar, Jan Peter Balkenende ya yi a ran juma’ar da ta wuce, sakamakon saɓanin da ya ɓarke tsakanin jam’iyyarsa da jam’iyyar D66 da ke cikin gwamnatin haɗin gwiwar da yake yi wa jagoranci. A halin yanzu dai Sarauniya Beatrix, ta naɗa tsohon Firamiyan ƙasar, Ruud Lubbers, da ya naɗa sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya har zuwa lokacin zaɓen.