1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben raba gardama a Libiya

Suleiman Babayo
December 6, 2018

Hukumar zaben Libiya ta ce za a gudanar da zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki a farkon shekara mai zuwa ta 2019 bisa matakin neman warware rikicin siyasa.

https://p.dw.com/p/39cRz
Parlamentswahlen in Libyen Al Bayda Wahllokal 25.6.2014
Hoto: Reuters

Shugaban hukumar zaben Libiya ya ce kasar da ke yankin arewacin Afirka za ta gudanar da zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki a karshen watan Fabrairun 2019. A wannan Alhamis shugaban hukumar Emad Al-Sayeh ya bayar da sanarwar a birnin Tripoli fadar gwamnatin kasar, abin da ke nuni da matakin farko na karkaka zaman lafiya da samun kwanciyar hankali na siyasa.

Hukumar zaben ta bukaci gwamnatin ta samar da makuden kudaden da ake bukata saboda zaben da ke tafe. Hakan ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin ta yi da sabon kundin tsarin mulkin wanda wani kwamiti na musamman mai mambobi 60 ya yi. Ita dai Libiya ta na fama da rikice-rikice tun shekara ta 2011 bayan kifar da gwamnatin marigayi shugaba Muammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.