1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a saurari karar cinikin jarirai a Nijar

Yusuf BalaNovember 26, 2014

Mutane 22 da ake zargi da hannu cikin badakalar cinikin jarirai a kasar ciki kuwa har da matar tsohon shugaban majalisar dokokin Nijar za su gurfana a gaban kuliya.

https://p.dw.com/p/1DuE3
Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Ministan harkokin shari'a a kasar ta Nijar Marou Amadou ya bayyana haka a ranar Laraban nan. Amadou ya ce wannan lamari na zargin cinikin jarirai da ke cike da sarkakiya abu ne da ke da sarkakiya da aka yi ta tafka muhawara a kansa. Amma nan ba da dadewa ba ne za a gurfana a gaban shari'a don kawo karshen lamarin. Sai dai bai bayyana ranar da za a saurari karar ba.

Ya ce mutane 22 an cajesu an kuma gabatar musu da jerin tambayoyi tun daga watan Yuni, sannan akwai ragowar shida da ake tsare da su kafin a gabatar da su gaban kuliya ciki kuwa har da babban wanda ake zargi.

Cikin wadanda ke hannun hukuma akwai matar Hama Amadou tsohon shugaban majalisar dokokin da ya fice daga kasar ta Nijar don neman mafaka a kasar Faransa.

Su dai wadanda ake zargin ana tuhumarsu ne da samun takardun shedar haihuwa na jabu da sauya wa yaran sunaye bayan safararsu daga wasu kasashe da suka hadar da Najeriya da Jamhuriyar Benin zuwa kasar ta Nijar.