1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a bawa sojin Iraki da na Kurdawa horo

Ahmed SalisuDecember 8, 2014

Kasashen da ke kawance da Amirka a yakin da ta ke yi da 'yan kungiyar nan ta IS sun amince da bada gudumawar soji dubu da dari biyar don bawa sojin Iraki da na yakin Kurdawa horo.

https://p.dw.com/p/1E182
Symbolbild USA Irak Truppen
Hoto: Lucas Jackson/AFP/Getty Images

Kwamadan sojin Amirka da ke jagorantar kawance da ke yaki da IS Lt. Janar James Terry ya ce nan ba da jimawa bane dukannin shirye-shiryen da ake za su kammala da nufin ganin sojin na raki da Kurdawa sun samu cikakken horon da suke bukata.

Iraki dai da Siriya da ma wani bangare na Turkiyya na daga cikin wuraren da yanzu haka suka fi fuskantar baraza ta 'yan IS wanda ke rajin girka daular Musulunci kuma yanzu haka ake fafatawa da su a garin nan na Kobani da ke kan iyakar Siriya da Turkiyya.