Tallafi ga kasashen da suka yi fama da Ebola
July 11, 2015Kasashen uku da suka hada da Liberiya, Gini da kuma Saliyo, za su samu wannan tallafi ne cikin shekaru biyu domin farfado da tattalin arzikinsu tare kuma da inganta harkokin kiwon lahiya. Tuni dai daga a nashi bangare shugaban kasar Gini Alhpa Conde, ya mika safifiyar godiyarsa a ranar Jumma'a a birnin New York ga kasashen da suka amince da bayar da wannan tallafi a yayin wani zaman taron kasashe kan bayar da tallafin da ya gudana a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin na New York.
Cutar ta Ebola dai ta yi sanadiyyar rasuwar mutane fiye da 11.200 daga cikin mutane 27.500 da suka kamu da ita, inda a Liberiya kadai mutum 4.800 suka rasu. Alpha Conde ya ce matsalar cutar ta Ebola tamkar matsala ce ta yaki kuma wannan mataki na bayar da tallafi ga kasashen da cutar ta fi kamari shi ne daidai domin su samu farfadowa.