Zaɓen gama gari a Saliyo cike da ƙalubale
November 17, 2012Al'umma na kaɗa ƙuria a zaɓen gama garin da ake gudanar wa a ƙasar Saliyo, inda kimani mutane miliyion biyu da rabi wanda suka cancanci zaɓe zasu zabi shugaban ƙasa da wakilan yan majalisu dokoki da kuma na ƙananan hukumomi.
Masu aiko da rahotanin sun ce ko'ina a cikin birnin Freetown babban birnin ƙasar jama'a sun ja dogon layi a bakin runfunan kaɗa ƙuria.Zaɓen wanda wani zakaran gwanji dafi ne na dimokaradiyya ga ƙasar da ta yi fama da yaƙin basasa na kusan shekarun goma.
Yan takara guda tara ne zasu fafata a ciki hada shugaban mai barin gado Ernest koroma wanda ke kan mulki tun shekarun 2007.Masu lura da al'amura yau da gobe na cewar ba mammaki ɗan takarar jam'iyyun siyasar na addawa Julius Maada Bio ya taka rawar gani , ko da shi kema ma ana hasashe cewa Koroman shi ne zai lashe zaɓen.
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu