1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arewacin Najeriya na fuskantar barazanar 'yunwa

Ramatu Garba Baba MAB
July 31, 2021

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan a dauki matakin ceto rayukan miliyoyi da ke fuskantar barazanar mutuwa a sakamakon matsananciyar 'yunwa.

https://p.dw.com/p/3yM1M
Südsudan Kandak 2018 | Frau & Sorghumhirsen nach Essensabwurf WFP
Hoto: Sam Mednick/AP Photo/picture-alliance

Watanni uku masu zuwa, za su kasance lokacin da wasu sassan duniya za su fuskanci matsananciyar 'yunwa, kamar yadda wani sabon rahoton hadin gwiwar da Hukumar Abinci ta Duniya WFP da Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO suka fitar ya nunar.

Wuraren da suka fi fuskantar hadari, sun hada da yankin Tigray na kasar Habasha da Kudancin kasar Madagaska da Yemen da Sudan ta Kudu da kuma arewacin Najeriya. Baya ga su, akwai kasashen Afghanistan da Burkina Faso da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da jamhuriyar Dimukaradiya Kwango da Kolombiya da Haiti da matsalar za ta shafa a yayin da Somaliya da Nijar ke fuskantar matsalar karancin abinci. 

Mutum sama da miliyan arba'in ne ke fuskantar barazana na tsananin yunwa da ke bukatar taimakon gaggawa don ceto rayukansu inji hukumomin biyu. Sun nemi taimakon kasashen duniya masu karfi don shawo kan wannan damuwar kafin lokaci ya kure.