Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kulla yarjejeniya a Libiya
August 9, 2019Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana mai fatan samun cimma wata kwarya-kwaryar yarjejeniya daga bangarorin biyu da ke yaki da makamai a yau din nan, tare da fatan soma aiki da yarjejeniya tun daga gobe Asabar har zuwa karshen bukukuwan na babbar sallah.Tun a cikin watan Aprilun wannan shekarar ne sojojin da ke biyayya ga madugun yaki Khalifa Haftar suka yunkuri aniyar kwace iko da birnin Tripoli a hannun gwamnatin hadin kan kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, rikicin.