1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin dawo da masarautun gargajiya a Libiya

Mahmud Yaya Azare SB/LMJ
January 19, 2023

A kasar Libiya an fara wani sabon yunkurin dawo da masarautun gargajiya da tsohon shugaban kasar Marigayi Muammar Gaddafi ya rusa fiye da shekaru 50 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4MQ4V
Birnin Tripoli na Libiya
Sojojin LibiyaHoto: Yousef Murad/AP Photo/picture alliance

Bayan fiye da shekaru goma da tsundumar da Libiya ta yi cikin halin rashin tabbas sakamakon gazawar da 'yan siyasa da shuwagabanin kabilu suka yi wajen warware rikicin kasar da samar mata kyakkywan makoma, yunkurin farfado da tsarin mulkin sarakunan gargajiya da Kanal Muammar Gaddafi ya tunbuke tun kusan shekaru 50 da suka gabata, na kara kankama a kasar.

Zanga-zanga a Libiya
Zanga-zanga a LibiyaHoto: Hazem Ahmed/REUTERS

Jawabin da Yarima mai jiran gadon mulkin na Libiya da ke gudun hijira a kasar Birtaniya, Muhammad Ridha Sunusi ya yi wa 'yan kasar ta Libiya a farkon sabuwar shekara, albarkacin cika shekaru 70 da samun 'yancin kai daga mulkin mallakar Italiya, shi ya sake tayar da tsimin masu wannan ra'ayin komawa kan tsarin mulkin sarakunan gargajiyar, yadda a cikin jawabinsa, ya tuna musu cewa, har yanzu fa shi ne halattacen Sarkin Libiya, muddin za a ci gaba da amfani da kundin tsarin mulkin kasar da aka dawo da aiki da shi tun bayan juyin-juya halin da akai wa Kanal Gaddafi shekaru 11 da suka gaba:

Tuni dai kungiyoyin matasan da ada suka jagoranci zanga-zangar juyin-juya hali a kasar, suka amsa wannan kiran na Yarima mai jiran gadon, Muhammad Ridha Sunusi yadda sukai ta shirya taruka mabanbanta tare da yin bitar kundin tsarin mulkin samun 'yancin kai da aka dawo da yin aiki da shi a kasar shekaru 12 da suka gabata, don tabbatar da cewa, zai iya biya musu burace-buracen da suka jima suna hankoransa na samarwa kasar da zaman lafiya da adalci gami da ci-gaba.

Masu adawa da tsarin dai da suke ganin zai mayar da kasar zamanin mulkin mulukiya da ake bautar da 'yan kasa, na zargin cewa shugaban gwamnatin hadakar kasar Abdulhameed Dibaiba ne da ya tabbatar tasa ta kare, yake kokarin jawo yamutsin da zai ba shi damar dorewa kan mulki, wanda ya yi ammanar cewa yunkurin farfado da mulkin gargajiyar mafarki ne dai yi wuya ya tabbata.