1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin Cocin Katolika na sasanta rikicin Kamaru

Abdul-raheem Hassan
May 8, 2018

'Yan Kamarun na da fatan cewar cocin Katolikan zai iya taka rawa wajen warware rikicin da ke haddasa asarar rayuka a yankin masu magana da Turancin Ingilishi.

https://p.dw.com/p/2xN1N
Vatikan kamerunischer Präsident Paul Biya trifft Papst Franziskus
Hoto: Getty Images/AFP/V. Pinto

Tun lokacin da rikici ya barke a yankin Kamaru masu magana da harshen Turancin Ingilishi ne dai aka baza jami'an tsaro a ko'ina. Manyan motoci dauke da jami'an tsaro na sintiri cikin dare a yankin. Wani dan jarida da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce tamkar sun koma karkashin mulkin soji ne. Ana kame mutanen da ake zargi da kasancewa cikin rundunar masu fafutukar nemarwa Ambazoniya 'yanci ana bindigesu ba tare da gurfanar da su gaban shari'a ba.

Deutschland Demonstration gegen die Unterdrückung von Minderheiten in Kamerun
'Yan Kamaru mazauna Jamus na zanga zangar kafa yankin AmbazoniyaHoto: picture-alliance/ZumaPress

" Wannan hadin baki ne tsakanin sojoji da sashin shari'a. Batu ne da ake gudanarwa da yawun babban mai shari'a na kasa da majalisar gudanarwa. Duk su na da masaniya dangane da wannan batu. Su na bayar da umurni ne kawai ga jami'an tsaron, su kuma nan take sai su zartar da umurnin ta jhanyar bindigewa. Ana samun kudi mai yawa ta hanyan wannan rikici".

A shekarun 1960 Kamaru ta samu 'yancin kai, lokacin da aka hade yankunan da ke karkashin Faransa mai magana da harshen Faransanci da yankunan da ke magana da harshen Ingilishi. A hukumance dai kasar na amfani da harsuna biyu watau Turanci da Faransanci. Sai dai daidaikun mazauna yankin Kudu masu yammaci masu magana da harshen Ingilishi na ganin cewar an dannesu a ko wane fanni. Tun a shekarar 2016 ne rikicin tawaye ya fara a yankin da zanga zangar lauyoyi, kana malamai suka bi baya kafin na al'umma. Kana a shekara ta 2017,  bore da yajin aiki suka biyo baya.

Kamerun Paul Biya
Shugaban aksar Kamaru Paul BiyaHoto: picture alliance/abaca/E. Blondet

Paul Biya da ke mulkin kasar tsawon shekaru 35 ya na da hukumar da ta kunshin harsunan biyu don warware matsalar, sai dai bangaren masu magana sun ce hakan bai wadatar ba. Asarar rayukan jami'an gwamnati da na tsaro da ma al'umma, ya jagoranci shugaban kasar kaddamar da yaki a kan 'yan awayren.

Sai dai Kungiyar sasanta rigingimu na kasa da kasa ta nemi majami'ar darikar Roman katolika da ya shiga tsakani, ganin cewar ko wane mutum daya daga cikin uku a kasar dan darikar ne. Emmanuel Busho, Bishop ne a Buea. Ya ce "Na amince, sai dai lamarin na da wuya a cikin wannan yanayi da ake ciki."

Bishop Busho ya ce gwamnati ta gindaya wasu ka'idoji na zama teburin sulhun, wanda a ganinshi hakan bai dace ba idan har ana son gano bakin zaren warware wannan matsala.