1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Houthi na tattauna batun tsagaita wuta

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 4, 2015

Kungiyar 'yan Houthi ta Yemen ta ce ta na tattauna batun yiwuwar tsagaita wuta a yakin da suke gwabzawa a kasar albarkacin watan azumin Ramadan da muke ciki.

https://p.dw.com/p/1FsoO
Yara kanana da suka shiga halin tasku a Yemen
Yara kanana da suka shiga halin tasku a YemenHoto: picture-alliance/AA/M. Hamoud

Kungiyar tace ta na tattauna batun ne tare da Majalisar Dinkin Duniya domin bayar da damar kai kayan agaji ga wadanda yakin ya tagayyara. Kakakin kungiyar ta Houthi Mohammed Abdul Salam ne ya sanar da hakan a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook, inda ya ce ya gana da babban jakadan Majaliar ta Dinkin Duniya a Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmed domin tatauna batun. Tun dai cikin watan Mayun da ya gabata ne kasar Saudiya ta fara jagorantar sauran kawayenta kasashen Larabawa wajen yin ruwan bama-bamai a kasar ta Yemen a abin da suka kira kokarin kare halastacciyar gwamnati karkashin Shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi da a yanzu haka ya ke gudun hijira, da ga mamayar 'yan Houthi da suke zargin kasar Iran da mara musu baya.