Yawan mutanen da Ebola ta kashe ya haura 2.000
September 5, 2014Talla
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar Ebola yanzu ya haura mutum 2.000, musamman a kasashen nan uku da ke yankin yammacin Afirka. Hukumar ta ce baya ga mutane 2.097 da cutar ta yi ajalinsu a kasashen Guinea da Liberiya da kuma Saliyo, mutane takwas sun kwanta dama a Najeriya, inda cutar ba ta yadu sosai ba. Hukumar ta WHO ta kuma tabbatar da yawan mutane kusan 4.000 da suka harbu da kwayar cutar a kasashen da lamarin yafi muni, sannan a Najeriya yawansu ya kai mutum 23, daya kuma a kasar Senegal. A kuma halin da ake ciki kungiyar Tarayyar Turai ta kara yawan taimako a yakin da ake yi da Ebola a yammacin Afirka, ya zuwa Euro miliyan 140.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman