1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma sulhu a Sudan ta Kudu

Mohammad Nasiru Awal GAT
August 6, 2018

Bayan shekaru na yakin basasa a kasar Sudan ta Kudu, bangarorin da ke rikici da juna a kasar sun amince da yarjejeniyar raba madafun iko.

https://p.dw.com/p/32gko
Uganda Südsudan - Friedensgespräch zwischen Präsident Kiir, Oppositionsführer Machar und der ugandische Präsident Museveni
Musabihar Shugaba Kiir na Sudan ta Kudu da abokin hamayyarsa Machar a gaban Shugaba Museveni na Yuganda.Hoto: Getty Images/AFP/S. Sadurni

A ranar Lahadi Shugaba Salva Kiir da babban mai adawa da shi kuma tsohon mataimakinsa, Riek Machar hade da wani kawancen kungiyoyin tawaye suka rattaba hannu kan gagarumar yarjejeniyar zaman lafiyar. 

A Khartoum babban birnin kasar Sudan aka yi bikin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ta kasar Sudan ta Kudu. A gaban idon shugabanni da dama na Afirka, Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da abokin hamayyarsa Riek Machar suka sanya hannu kan yarjejeniya da ta tanadi tsagaita bude wuta da raba madafun iko kamar yadda Shugaba Kiir ya yi karin gaske.


"Dole mu fada wa kanmu gaskiya, mu kuma amince cewa wannan yakin basasa da mu 'yan Sudan ta Kudu muka kwashe shekaru biyar muna yi, ba shi da ma'ana, ya jefa al'ummarmu cikin hali mawuyaci, da kashe-kashen daruruwan matasa maza da mata, na ba bu gaira ba bu dalili. Ya lalata tattalin arzikinmu ya kuma raba kan kasarmu da al'ummarmu fiye da a lokutan baya."

Südsudan Rebellen
Mayakan tawayen Sudan ta KuduHoto: Getty Images/AFP/C.A. Lomodong

Ana sa rai nan da watanni uku a kafa majalisar ministoci ta rikon kwarya da za ta yi mulki tsawon shekaru uku. Shugaba Kiir zai ba da sunan mutum 20, Riek Machar mutum tara sannan guda shida za su fito daga sauran kungiyoyi. Za a sake ba wa Machar mukamin mataimakin shugaban kasa. An kuma amince da kafa majalisa mai wakilai 550, 332 daga Kiir, 128 daga Machar, ragowar kuma daga sauran kungiyoyi. Za a fadada yawan wakilai na shugabancin kasar domin biyan bukatun kowane bangaren na al'umma. Sai dai tambaya a nan ita ce samar da kudin tafiyar da aikinsu, kasancewa Sudan ta Kudu duk da arzikin man fetur, tana fama da talauci sakamakon shekaru na yakin basasa. Saboda haka Shugaba Kiir da Machar suka yi kira da a aiwatar da yarjejeniyar,a cewar Riek Machar.

"A wasu lokutan akwai matsala wajen aiwatarwa. Idan ba bu wani kuduri na siyasa, za mu iya sanya hannu kan yarjeniyoyi masu kyau, amma ba za mu samu sukunin aiwatar da su. In mun yi haka ai ba mu cimma komai ba."

Shugaba Kiir na da kyakkyawan fatan wannan yarjejeniyar za ta dore domin kuduri ne na masu rikici da juna, amma ba matsin lamba ne daga waje ba.

Sudan Khartum Abkommen zur Machtteilung im Südsudan unterzeichnet
Shugaba Kiir na Sudan ta Kudu na saka hannu kan yarjejeniyar sulhu.Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Sai dai duk da haka masharhanta sun nuna damuwa cewa akwai muhimman batutuwa da yarjejeniyar ba ta kunsa ba. Brian Adeba shi ne mukaddashin daraktan Kungiyar Policy for the Enough Project da ke birnin Washington na kasar Amirka, mai burin ganin an kawo karshen cin zarafin dan Adam.


"Yarjejeniyar ta bambanta ta kuma samu karbuwa daga dukkan bangarorin da ke rikicin, sai dai ba ta cika ba, domin ba ta warware dukkan matsalolin da ke kasa ba, musamman na raba kudaden kasa da yi wa sashen tsaron kasa garambawul."

Wannan dai shi ne karo na biyu na kokarin amfani da matakin raba madafun iko don kawo karshen yakin basasa. Makamanciyar wannan yarjejeniya da aka kulla shekaru biyu baya ta ruguje. Yanzu karo na 12 kenan ana amincewa da shirin tsagaita wuta a kasar ta Sudan ta Kudu.