'Yan tawayen Syria sun shiga birnin Aleppo
November 29, 2024Talla
Rami Abdelrahman shugaban kungiyar sa ido don kare hakkin al'umma a Syria ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa cewa 'yan tawayen sun shiga cikin Aleppo karon farko tun shekarar 2016
A halin da ake ciki sojojin Syria sun fada a cikin wata sanarwa cewa rundunar sojin gwmnatin sun kwace iko da wasu muhimman wurare da aka sami tashin hankali kuma za su ci gaba da yaki har sai sun fatattaki 'yan tawayen.
Sojojin sun kuma zargi 'yan tawayen da yada labaran karya domin hargitsa al'umma.
Fadan ya tilasta wa mutane kusan 14,000 barin muhallansu a cewar Majalisar Dinkin Duniya.