1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan tawayen Kwango sun kashe fararen hula da dama

April 7, 2024

Wani daftarin rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya tattabar da mutuwar karin wasu mutanen 25 a yayin wani mummunar hari da 'yan tawaye suka kai wani kauye a lardin Ituri da ke gabashin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/4eWKC
'Yan tawaye a yayin wani rangadi a Kwango
'Yan tawaye a yayin wani rangadi a Kwango Hoto: Moses Sawasawa/AP Photo/File/picture alliance

Wasu 'yan tawaye da ake yiwa lakabi da (CODECO) sune suka kaddamar da harin kan kauyen Galayi da ke da nisan mile 45 daga arewa maso yammacin birnin Bunia, acewar shugaban kungiyar da ke fafutukar kare hakkin 'dan adam a yankin.

Karin bayani: Kwango: Sabon rikici a arewacin Kivu 

Ya ce an samu karin gawarwaki idan aka hada da alkaluman wadanda aka samu  guda 10 a jiya asabar, kamar yadda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Karin bayani: Rikici ya halaka mutane a Kwango 

Al'amuran tsaro na sake tabarbarewa a yankin na Ituri tun bayan kaddamar da hare-haren kan mai uwa da wabi da 'yan tawayen (CODECO) sukayi, kamar yadda wani rahoton hukumar kare hakkin 'dan adam na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar a wani rahoton hadin gwiwa da kungiyoyin kare hakkin 'dan adam na yankin.