'Yan tawaye sun kashe sojojin Mali
April 6, 2020Rahotannin da ke fitowa daga Bamako babban birnin kasa ta Mali, sun tabbatar da mutuwar dakarun kasar akalla 20 a wani hari da mayakan tarzoma suka kaddamar a kansu, kamar yadda wasu majiyoyi ciki har da na tsaro suka nunar.
'Yan bindigar sun afka wa sansanin dakarun gwamnatin na Mali ne da ke garin Bamba a yau Litinin, a sabon farmakin da sojin suka gani.
Wani jami'in gwamnati a yankin, ya ce an dai sami asarar rayuka daga bangarorin duka biyu, sai dai bai bayyana adadin 'yan bindigar da sojojin suka kashe ba.
Tun cikin shekara ta 2012 ne dai Malin ke fama da matsalolin tsaro, sakamakon hare-haren 'yan bindigar da ke da'awar jihadi, inda dubban 'yan kasar da ma sojoji suka salwanta, duk da kasancewar rundunar samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a can.