1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe dan jaridar Pakistan bisa kuskure

Zainab Mohammed Abubakar
October 24, 2022

'Yan sanda a Kenya sun kashe wani shahararren dan jaridar Pakistan da ke buya a kasar, saboda motar da ya ke tafiya a ciki ta ki tsayawa a wani wurin binciken jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/4Ic9W
Pakistanischer Journalist Arshad Sharif
Hoto: AP/picture alliance

'Yan sanda a Kenya sun kashe wani shahararren dan jaridar Pakistan dake buya a kasar, saboda motar da ya ke tafiya a ciki ta ki tsayawa a wani wurin binciken jami'an tsaro a kusa da birnin Nairobi.

Sun sanar da cewar kisan nasa kuskure ne, saboda motarsu ta yi kama da wadda ake zargi da sace yaro kuma ana nemata.

Mai shekaru 50 da haihuwa, Arshad Sharif yana buya ne a Kenya, bayan tserewa barazanar kama shi a watana Juli, saboda sukar rundunar sojin kasar ta kudancin Asiya mai karfin iko.

'Yan sandan Nairo bi sun sanar da cewar, Sharif ya mutu ne sakamakon harbinsa a kai jiya da daddare, lokacin da motar da ya ke tafiya a cikinta da dan uwansa Khurram Ahemed ta shige a guje ba tare da tsayawa a inda jami'an tsaro ke binciken ababén hawa a kan babban titin  Nairobi zuwa Magadi.