An kashe wadanda suka yi wa likita fyade
December 6, 2019Matakin da 'yan sanda a kasar Indiya suka dauka na harbe wasu mutane hudu da ake zargi da yi wa wata Likitar dabbobi fyade kafin su kashe ta, ya janyo ra'ayoyi mababanta a kasar. A dai safiyar wannan Jumma'ar ce, fada ya barke a tsakanin jami'an 'yan sandan da wadanda ake zargin bayan da suka yi yunkurin kwace makamai daga hannunsu, lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake binciken tabbatar da laifin a kan matasan.
N Prakash Reddy shi ne mukaddashin 'yan sandan birnin Hydrabad da ke jagorantar binciken, ya ce, akwai jami'ansu biyu da suka ji rauni a yayin hatsaniyar. Babu dai cikakken bayani daga mahukunta kan yawan jami'an tsaron da ke rakiyar masu laifin a yayin da rikicin ya barke. Iyalan matar mai shekaru 27 da haihuwa dama sauran al'umma musamman wadanda ke hakilon ganin an kawo karshen cin zarafin mata sun nuna gamsuwarsu, a yayin da wasu ke ganin bai dace 'yan sandan su dauki doka a hannunsu ba.
Matsalar fyade da ake yi wa mata a Indiya, na ci gaba da jan hankulan kungiyoyi masu rajin kare hakkin mata ba tare da an iya shawo kanta ba. A shekarar 2017 kadai, mata sama da dubu talatin da biyu aka yi wa fyade a Indiya.