Najeriya: An kashe shugaban jam'iyyar APC a Zamfara
February 23, 2019Talla
A Jihar Zamfara, wasu 'yan bindiga sun hallaka Alh Yusuf Agege, shugaban jam'iyyar APC a gundumar Yandoto, kakakin rundunar 'yan sandan Jihar, SP Shehu Muhd ya tabbatar da afkuwar lamari a wata sanarwa da ya bayyana. Wanda ya ce maharan sun bude ma shugaban jam'iyyar wuta inda nan ta ke ya rasa ransa. Haka kuma maharan sun so su kawo cikas a wasu runfunan zabe a jihar a yayin zaben na wannan Asabar sai dai hakan bai samu nasara ba.