Zanga-zanga a yakin Kashmir
September 25, 2015Talla
'Yan sanda a kasar Indiya sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa wasu gungun mutane da ke gudanar da wata zanga-zanga don nuna kin jinin gwamnatin kasar Indiya. 'Yan sanda a kasar Indiya sun yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga zangar a yankin Kashmir da ke bangaren yankin Kasmir.
Wani dan sandan kasar Indiyan ya fadawa manema labarai a yau jumma’ar nan cewar masu zanga -zangar na kada tutoci kasar Pakistan da kuma tutar mayakan sa kai gami da jefa duwatsu akan jami’an tsaron gwamnatin Indiyan, a dai dai lokacin da ke suke kokarin hanasu zanga- zangar a Srinagar tare da Karin wasu gurare biyu a yakin.